SERIES: Rahama Sadau’s Amaryar Lalle Series Zai Fara a Ranar Talata!

Amaryar Lalle Series
Amaryar Lalle Series

Duk da jira da masu kallo suka yi, yanzu dai ga ta nan. Shahararriyar jaruma kuma producer, Rahama Sadau, a karshe ta bayyana cewa sabon fim dinta na Amaryar Lalle Series zai fara haskawa a ranar Talata, 12 ga Agusta, 2025, da misalin karfe 8:00 na dare. Wannan sanarwar ta zo ne bayan fitar da wakar soundtrack din fim din mai taken “Amaryar Lalle” daga mawaki Umar M Shareef, wanda ya kara tada hankulan masoya. Ana sa ran za a haska fim din a tashar YouTube ta Rahama Sadau TV.

Cikakken Bayani:

  • Darakta: Dan Hausa
  • An Shirya Shi: Rahama Sadau da Sadau Pictures
  • Ranar Farko: Talata, 12 ga Agusta, 2025 (8:00 PM)
  • Za’a Kalla A: YouTube (Rahama Sadau TV)
  • Manyan Jarumai: Umar M Shareef, Rahama Sadau, Rukky Alim, Suhailat Ishaq, Baba Sadieq, Official Meerahhh, da Yusuf Lazio.

An riga an saki Trailer na fim din a tashar YouTube, wanda ya nuna tsananin basirar da ke tattare da fim din da kuma jajircewar ‘yan wasan da suka ba da gudummawa.

Kalli Trailer Anan:

Kada ku manta ku shirya tsaf domin ranar Talata don kallon farawa na wannan jerin fim, sannan ku ajiye mana ra’ayoyinku a Æ™asa idan kun kalla.

FAST DOWNLOAD NOW

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*