
Sabon labari mai ɗauke da abun tausayi na tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood, Ummi Nuhu…
A jiya ne Yuli 24, 2025 tashar Hadiza Gabon tayi wata tattaunawa da wata tsohuwar jarumar masana’antar fim ta Kannywood wato Ummi Nuhu a ɗakin shirin ta na Gabon Room Talk Show. Inda jarumar ta faɗi irin ƙalubalen da suka faru da ita.
Wanda take cewa tana matukar son harkar fim domin ita kaɗai ta sani a rayuwarta. Amma a duk lokacin da ta nemi a sakata acikin fim sai abun yazama abun ɓacin rai, hakan yasa kowa yake gudunta saboda irin kuskuren da ta aikata a baya.
Ga abinda tace a ƙasa;
Ganin yanda Ummi Nuhu ta fito ta faɗi irin abubuwan da suka faru da ita a rayuwa haka yasa mutane da dama kowa a kafafan sada zumunta sai magana ake akan irin halin da take ciki a yanzu.
Aikuwa nan da nan sai wata daga cikin fitattun jaruman masana’antar Kannywood wato Momee Gombe ta wallafa wani rubutu a shafinta na instagram inda take cewa;
Ni daku ƙawaye na mu kiyaye rayuwa mu sani cewa komai lokaci ne, ya Allah yadda muka fara lafiya Allah kasa mu gama lafiya. Amma dan Allah muyi ƙokari mu gyara kodan saboda rayuwa bata da tabbas. Idan maganata ta batamuku daɗi ba ƙawaye na kuyi haƙuri 🙏😭 dan Allah kutai maka mata.
Bayan tayi wannan rubutun sai tayi tagging na wasu daga cikin manya a masana’antar fim ta Kannywood irin su Ali Nuhu, Abdulsmart Mai Kwashewa, Real Maishadda, Yakubu Muhammad, Abba El-Mustapha.
kamar yanda zaku gani haka;

Me kuke gani game da wannan lamari? Shin da gaske irin waɗannan kalubalen suna yawaita a Kannywood?
Ku bar mana ra’ayinku a sashin sharhi da ke ƙasa!
To sai muce Allah ya kiyaye, Kuma wannan yazama Aya ga wadanda suke tashe a yanzu su natsu su hankalta Susan cewar ita masa’antar kanywood tabi’arta Daya da duniya yar dauki aje ce
Ameen ya Allah 🙏