Matar Da Ta Rungumi Mawaki Soja Boy Ta Fito Ta Tona Asirin Sa

Wata sabuwa cikin wata sanarwa da matar da ta rungumi Soja Boy ta fito ta tona asirin sa a wani sabon bidiyo daya fito.
Idan zaku iya tunawa kwana biyu da suka wuce mawaki Soja Boy ya saki wata sabuwar wakarsa ta soyayya mai suna “Bugun Zuciya” inda wakar tasamu karbuwa a manhajar TikTok saboda irin dadin data yi.
Kawai sai lokaci daya akaga mawaki Soja Boy da jarumin TikTok wato Itx Lawancy sun saki wani bidiyo inda mawakin Soja Boy yake rungumar matar dake cikin wakar wanda hakan yajawo cece-kuce akafar sada zumunta.
Shine yanzu kuma a wani sabon bidiyo daya fita matar da Soja Boy ya runguma tace babu wani kudi da yake dashi idan kuma yana dashi ya fito ya fadi nawa yataba turamata wanda yanzu haka zaku iya kallon cikakken bidiyon da take bayani.
Source: DDL Hausa