News

An Ɗaura Auren Ahmed Xm Da Safeera Abba

Cikin ikon Allah dai an daura auren Ahmed Xm da Safeera Abba a ranar Juma’ar da ta gabata wato 31-01-2025.

Idan zaku iya tunawa Ahmed Xm da Safeera sun jima suna soyayya wanda har takama duk inda wani zaije daga cikin su toh zaka gansu tare saboda tsananin yanda suke son junan su.

Duk wannan soyayyar da suke da irin shakuwa da juna da sukayi sai lokaci daya kuma akaga Ahmed Xm zai aure wata yarinya wato Safiyya wanda hakan yajawo cece-kuce sosai akafafan sada zumunta.

Inda wasu daga cikin mutane suke cewa; Maganar gaskiya Ahmed Xm yaci amanar Safeera duk irin soyayyar da sukayi da ita ashe yaudararta kawai yake. Haka mutane su kai ta magana har saida akayi auren Ahmed Xm da Safiyya.

Wanda yanzu har anyi shekara daya da yin auren Ahmed da Safiyya cikin ikon Allah kuma har sun samu karuwa da ita.

Ahmed Xm Da Safiyya

Sai kuma yanzu aka ji cewa Ahmed Xm zai auri Safeera wanda mutane sun yi matukar mamaki har saida aka kasa gane mene gaskiyar alamarin wannan yasa wasu daga cikin mutane suka fara cewa karyane wasu kuma suna cewa dagaske ne.

Duk da cewa Ahmed Xm da Safeera basu wani nuna wata alama tacewa zasuyi aure ba. Domin babu wani daga cikinsu da ya saka wata alama da har za’a gane cewa zasuyi aure.

Amma wasu daga cikin abokan Ahmed Xm irin su Anikstar duk sun saka bidiyo na shaidar cewa Ahmed zai yi aure. Dama ance abin duniya baya buya duk cewa anyi abun ne aboye amma hakan baisa auren yabuya ba.

Yanzu dai zancen da ake an daura auren Ahmed Xm da Safeera inda wasu daga  cikin mutane suke yi musu fatan alkhairi na Allah yabasu zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!