News

Nayi Nadamar Taɓa Hannu Da Fuska Na Wacce Ba Maharramata Ba – Bilal Villah

FAST DOWNLOAD MP3

Matashin mawaki mai tasowa wato Bilal Villah yace; nayi nadamar taba hannu da fuska na wacce ba maharramata ba.

Idan zaku lura a kwana biyun nan ne kawai akaga mawaki Bilal Villah da wata sabuwar yarinya acikin wani fefan bidiyo a shafin sadarwa na TikTok inda yake taba mata hannu da fuska da sauransu wasu abubuwa da dama.

Wannan abu dai ya jawo cece-kuce inda wasu da dama daga cikin mabiyansa suke cewa; wannan abu da kake gaskiya bai kamata ba ace yarinya karama kana kokarin zaka lallatata.

Haka dai mutane su kaita tofa albarkacin bakin su akan abinda Bilal Villah yayi wanda yanzu haka zaku iya kallon kadan daga cikin bidiyon.

Ganin yanda mutane suke magana mawaki Bilal Villah a yau laraba ya sanarda da cewa akan story dinsa na TikTok cewa; “Assalamu alaikum Ina mebada hakuri akan abubuwan da yafaru jiya zuwa shekaran jiya akan taba hannu da fuska na wacce ba maharramata ba, kuma insha Allah hakan bazai kara faruwa ba nagode

Me zaku iya cewa akan wannan abu na mawaki Bilal Villah ku ajiye mana a comment section

FAST DOWNLOAD MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!