News

Na Daina Gabatar Da Shirin BREKETE FAMILY Na Hausa – Ordinary President Ahmad Isah

Akwai yiwuwar na daina gabatar da shirin Brekete Family na Hausa cewar Ordinary President Ahmad Isah cikin wani martani daya mayarwa da mutane masu cece-kuce akansa tun bayan fitar bidiyon maganar Hussaina matar Seaman Abbas.

Ahmad Isah ya fito ya sanarda hakane ganin yanda mutane suke ta maganar cewa ya cuci Hussaina matar Seaman Abbas. Saboda mutane tun abaya sun yi niyyar zasu taimaka mata amma yace ba haka ba.

Wannan maganar ta dauko asaline bayan Hussaina a wani bidiyo ta fito tace; ita fa mota da akace za’a bata da kuma 20 million har yanzu ba’a bata ba. Kuma gashi ni a yanzu bani da lafiya mijina ma danake tare dashi yanzu bama tare.

Takara da cewa a yanzu babu abinda nake bukata irin addu’ar mutane ganin irin halin da nake ciki da kuma rashin jin dadi.

Aikuwa babu wani jira mutane a kafar sada zumunta ta TikTok dasauran manhajojin sadarwa suka fara mayarwa da Ahmad Isah martini akan yacuci Hussaina babu wani abu daya taimake ta dashi.

Duk da cewa mutane basu bari sun ji ta bakinsa ba suka fara maganar babu wani abu daya taimake ta dashi.

Wannan shine dalilin daya jawo wannan magana da Ahmad Isah yace zai daina gabatar da shirin Brekete Family na Hausa.

Wanda yanzu haka zaku iya ganin kadan daga cikin maganar tasa a wani bidiyo daya saka zakuma ku iya samun cikakken bidiyon a youtube channel ta Brekete Family.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button