
Barka da zuwa HausaTracks.com! Kwanan nan masana’antar Kannywood ta sake shiga wani yanayi na cece-kuce da ake ta muhawara a kafafen sada zumunta. Wannan lamarin ya haɗa da fitattun jarumai mata guda uku: Saima Muhammad, Ummi Nuhu, da kuma Rashida Mai Sa’a. Labarin dai ya faro ne daga wata magana mai cike da dabara daga bakin Saima Muhammad, wacce ta jawo martani mai zafi daga Rashida Mai Sa’a, dake kare Ummi Nuhu. Ku biyo mu don jin cikakken bayani!
Magana Mai Zafi Daga Bakin Saima Muhammad: Shin Wacece Take Nufi?
Lamarin dai ya fara ne da wani bidiyo da jaruma kuma tsohuwar tauraruwar Kannywood, Saima Muhammad, ta wallafa a shafinta na TikTok. A cikin bidiyon, Saima Muhammad ta ba da wata shawara mai muhimmanci ga al’umma, inda ta ce:
Shawara ce da ita nake so zan bayar kyauta. Na ɗaya dai, in dai har kana so ka gama da duniya lafiya, to ka bi iyayenka. Duk abin da suke so, ka dinga yi musu. Shine ta ƙara da cewa, ka zauna da su lafiya, kada ka zauna da su lafiya, wannan matsalar mutum ce. Amma idan baka zauna da su lafiya ba, wallahi ƙarshen mutum ba zai yi kyau ba. Don haka, ayi ƙoƙari a zauna da iyaye lafiya.
Ga bidiyon daga kasa;
Duk da cewa Saima Muhammad bata ambaci sunan kowa kai tsaye a cikin maganar tata ba, nan take masu bibiyar shafukan sada zumunta suka fara hasashe. Yawancin jama’a sun yi imanin cewa maganar tana nufin jaruma Ummi Nuhu ne, ganin yadda labarai ke yawo game da wasu al’amura da suka shafi Ummi Nuhu a baya.
Rashida Mai Sa’a Ta Fito Da Gaskiya, Ta Kare Ummi Nuhu Gabakidaya!
Bayan da bidiyon Saima Muhammad ya yadu, wata tsohuwar jaruma kuma abokiyar aikinsu, Rashida Mai Sa’a, ba ta ɓata lokaci ba. Ita ma ta fito a shafinta na TikTok don yin martani, inda ta fara da bayyana cewa tana so ta yi magana akan mutane biyu.
Da take magana akan Saima Muhammad, Rashida Mai Sa’a ta bayyana cewa:
Na farko, Antinmu Saima Muhammad, ita uwa muka ɗauke ta. Saima Muhammad muna ganin mutuncinta da ƙimarta.
Bayan haka, Rashida Mai Sa’a ta shawarci Antinta Saima Muhammad da cewa:
Aunty Saima Muhammad a matsayinki na babba wacce koda wani abun kikaga yar uwarki yar fim bai kamata kishigo kiyi habaici da shagube acikin maganar ki ba, magana ta domin Allah.
A ƙarshe kuma, ta kare jaruma Ummi Nuhu gabakiɗaya, tana mai bayyana halin ƙoƙarin Ummi Nuhu wajen kula da mahaifiyarta:
Hakika ni Rashida Mai Sa’a nayi rayuwa da Ummi Nuhu yanda bakwa tunani. Kuma a maganar Gaskiya iya bakin ƙoƙari da ‘ya ko ɗa, nidai zaman danayi da Ummi Nuhu naga irin bakin ƙoƙarin datayi da mahaifiyarta.
Ga bidiyon daga kasa;
Menene Wannan Lamarin Ke Nufi ga Masana’antar Kannywood?
Wannan lamarin ya nuna yadda shahararrun mutane ke iya shiga cikin rigingimu na kafafen sada zumunta, wanda ke jawo cece-kuce tsakanin masu bibiya. Yana kuma nuna yadda abokan aiki ke iya shiga tsakani don kare juna ko bayyana ra’ayoyinsu.
Yaya kuke ganin wannan lamarin zai kare? Shin akwai gaskiya a maganar Saima Muhammad ko kuwa Rashida Mai Sa’a ce ke faɗar gaskiya game da halin Ummi Nuhu?
Muna gayyatar ku ku bayyana ra’ayoyinku a sashin comments a ƙasan wannan shafin. Kada ku manta ku ci gaba da bibiyar HausaTracks.com don samun sabbin labarai masu zafi daga Kannywood da kuma waƙoƙin Hausa mafi zafi!
Karanta: Martanin Momee Gombe Akan Kaddarar Ummi Nuhu a Kannywood
Leave a Reply