Kannywood

An dakatar da Jaruma Samha M Inuwa daga yin finafinai tsawon shekara guda

Hukumar tace fina-fanai ta jihar Kano ta dakatar da Jaruma Samha M. Inuwa daga fina-fanai har tsawon shekara guda saboda zargin yin shigar banza a wani bidiyo a yau asabar 01-04-2025.

Hukumar ta kara da cewa ba za ta kuma tace duk wani fim da Jarumar ta fito a ciki ba. Wannan sanarwar ta fito ne daga wani ma’aikacin gidan jarida na Freedom Radio Kano wanda aka fi sani da Basheer Sharfadi inda ya wallafa a shafinsa na facebook.

Shin wannan mataki da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dauka akan Jaruma Samha M. Inuwa ya yi daidai ku ajiye mana ra’ayinku a comment section.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button