News
Ƴan sandan jihar Kano sun yi nasarar kama wani Ɓarawon mota
Rundunar yan sanda ta jihar Kano ta kamo wani kasurgumin Barawon mota a garin Katsina a bisa bincike da yan sandan suka yi ya tabbatar musu da shine ya saci motar.
A safiyar yau litinin ne Hausa Tracks ta ci karo dawani labari daga wajen shugaban rundunar yan sanda na jihar Kano wato Abdullahi Haruna Kiyawa inda ya saka cewa “Ku nemo Yan Zaria suzo Birnin Kano mun samo motarsu da aka sace“.
Wannan barawo sunansa Bala Muhammad mai shekaru 40 a duniya kuma yana zaune a jihar Katsina inda yace asalin a Funtua yake wanda yanzu haka zakuji bayani daga bakinsa.