Iftihal Madaki: Yar TikTok da Ta Jawo Cece-Kuce Bayan Bidiyon Madox TBB

Wacece Iftihal Madaki?
Iftihal Madaki wata sabuwar yarinya ce da ta shahara a kafar TikTok saboda yawan bidiyoyinta da take yi cikin Hijabi. Wannan ya sa mutane da dama suka santa a matsayin yarinya mai tarbiyya da kamun kai, duk da cewa tana yin rawa ko wasa, to amma kullum tana rufe jikinta da Hijabi.

Fitowa a Wakar Namenj – Mun Kusa
Shahararren mawakin Hausa, Namenj, ya gayyaci Iftihal Madaki don ta fito a sabuwar wakarsa mai suna “Mun Kusa” wadda aka yi a Kaduna. Wannan ne karo na farko da mutane suka gan ta a cikin bidiyon mawaki. Bayan fitowar bidiyon, jama’a da dama sun yaba da irin kwalliyar da tayi da kuma yadda ta fito a cikin wakar.
Bidiyon da Ya Jawo Cece-Kuce
Bayan wannan nasara, sai ga wani sabon bidiyo da ya fito inda aka ga Iftihal tare da mawaka biyu: Madox TBB da kuma Sojaboy wanda ya shahara da wakar “Shafamata Nonowa.” A cikin bidiyon, Iftihal an ganta tana shafa jikin Madox TBB da irin salon da ake gani a gidajen rawa. Wannan ya ba mutane mamaki, ganin cewa a baya kullum tana cikin Hijabi ne a TikTok.
Martanin Jama’a
Wannan lamari ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta. Wasu suna ganin babu laifi, domin aiki ne na mawaka da bidiyo. Amma wasu kuma suna ganin hakan ya saba da irin hoton da ta gina a baya. Duk da haka dai, hakan ya kara daukar hankalin mutane, har sun sa sunanta ya fara fitowa a matsayin daya daga cikin abubuwan da ake yawan nema a Google.
Ko da yake ra’ayoyi sun bambanta, abu daya ya tabbata – Iftihal Madaki ta zama jigo a tattaunawar jama’a a yanzu. Masoya da masu suka duka suna jiran ganin matakin da zata dauka a matakin gaba na rayuwarta da harkar nishadi.